19 Maris 2026 - 16:52
Source: ABNA24
Ma'aikatar Leken Asirin Iran Ta Kama Maha’intar Kasar 111 A Fadin Kasar

Ma'aikatar Leken Asirin Iran ta gano adadi mai yawa na manyan bindigogi da kananan makamai na karfe daga waɗannan yan ta’adda.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: Har ila yau, an gano wasu 'yan leƙen asiri 4 na gwamnatin Amurka da sojojin hayarsu a Hamedan da Yammacin Azerbaijan. Wadannan 'yan leken asirin marasa kishin kasa sun ba da rahoto inda hedkwatar da kayan aiki da wurin da jami'an tsaro suke ga abokan gaba. Sannan a wani summen jami’an Iran sun Gano motar jigilar makamai guda biyu da aka shirya don amfani da su don haifar da tarzoma a kan titi, makaman da aka kama sun hada da bindigogi 29, Kalashnikovs 2 da ruwan wukake 58.

Sannan a wani binciken an gano tare da kama sojojin haya 21 da suke aika da bayanai da hotuna zuwa cibiyar ta'addanci ta International tare da gano manyan madaukar kayayyaki guda biyu na Starlink, 350,

A wani bangaren kuma an kama manyan manyan Yan ta'adda guda 75 a Alborz Wadannan mutane sun aika da hotunan wurare masu mahimmanci da aka kaiwa hari, sannan an kama wanda ya aikata laifin kade mutane da gangan da mota a cikin dare a Golshahr, Karaj, da sauransu a yayin tattaki, inda ya suka aike da kafar sadarwa mai adawa ta International.

Sannan an gano wadanda suka aikata laifin cinna wuta ga hotuna da cin mutuncin ga shahid jagora, da wasu masu tayar da kayar baya a sararin kafofin sada zumunci, da kuma mambobin wata kungiyar da ke da alaka na’urar Starlink.

Sannan an kama wasu maha’inta kasa su 41 a Alborz wadanda suke aika da bidiyo zuwa cibiyoyin sadarwar makiya a yakin Amurka da Isra'ila suke gundanarwa kan Iran. Daga farkon yakin zuwa yanzu an gano makaman farauta 2 da makaman yaki da alburusai 24 daga wasu masu laifi.

An kuma gano tare da kama "Sojojin hayar Isra'ila"  97 tare da kashe wani mashhurin mugun mutum dan ta’adda a kudu maso gabashin kasar.

A yayin wani aikin sashin kula da bayanan sirri na ma'aikatar leken asiri suka gudanar makiyin Amurka sun gano tare da kama sojojin hayar Isra’ila 97.

Wadannan mutane karkashin jagorancin abokan gaba na Amurka-Isra’ila, sun fara sun fara kafa cibiyar ta’addanci sun shirya don tarzoma a kan tituna da ayyukan ta'addanci da kashe-kashe, musamman na kwanakin karshe na shekara. Daga maboyar wadannan ‘yan ta’addan da aka yi hayarsu, an gano bindigogi 45 da alburusai da kananan makamai tare da lalata cibiyar.

Sannan an kama mutane 6 daga cikin kungiyar adawa ta Aran da Bidgol a daren Larabar karshe na wannan shekara.

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha